Mista Li ya ajiye kanbun fure a wuraren 2, gami da zaman makoki don tunawa da sojojin kasar Sin da suka mutu a yakin. Daga bisani ya bayyana cewa, shekaru fiye da 60 da suka wuce, sojojin kasar Sin sun yi yaki kafada da kafada da sojoji da jama'ar Koriya ta Arewa don kare kasashen 2, inda kokarinsu ya tabbatar da zaman lafiya da adalci.
A don haka inji shi Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, hukuma da jama'ar kasar, za su ci gaba da tunawa da Sinawan da suka sadaukar da rayukansu a yakin, da yadda suka kare kasar Sin da tabbatar da zaman lafiya bisa sadaukarwar su.
Ya kara da cewa, wani babban take na wannan zamani shi ne kiyaye zaman lafiya da neman samun ci gaba. Don haka, an yi bikin tunawa da yakin zirin Koriya ne don karfafa niyyar tabbatar da kwanciyar hankali a zirin, tare da samun walwala da ci gaba a wurin a nan gaba. (Bello Wang)