Hong Lei ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana. Ya ce, kasar Sin na ganin matakin gwajin makaman nukiliya da harbar tauraron dan adam da kasar Koriya ta Arewa ta yi, sun sabawa kudurorin kwamitin sulhun MDD, kana kwamitin sulhun yana da bukatar ya zartas da sabon kuduri, na hana karfin raya makaman nukiliya a kasar. Haka zalika kuma, kudurin ya sa kaimi ga bangarori daban daban da abin ya shafa, su mayar da batun nukiliya na zirin Koriya ya zamo hanya mafi dacewa ta sake gudanar da shawarwari a tsakanin bangarori shida.
Hong Lei ya kara da cewa, Sin tana fatan ci gaba da mu'amala tare da sauran kasashe. Kana idan har aka zartas da sabon kuduri, Sin za ta yi biyayya yadda ya kamata. (Zainab)