in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya da Turkiyya za su fadada hadin-gwiwa wajen yakar ta'addanci
2016-03-03 18:55:14 cri

Yayin da shugaban kasar Turkiyya Tayyip Erdogan ke ganawa da takwaransa na kasar Najeriya Muhammadu Buhari jiya Labara a birnin Abuja, ya ce Turkiyya za ta taimaki Najeriya da fadada hadin-gwiwa da ita ta yadda za a murkushe ayyukan ta'addanci.

Shugaba Erdogan ya yi wannan furuci ne ga manema labarai bayan da yayi wata ganawar sirri da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya.

Erdogan ya mika jajensa ga iyalan wadanda suka rasa ransu a cikin hare-haren ta'addanci da suka wakana kwanan baya a wasu sassan Najeriya. Ya kuma bayyana cewa, Turkiyyar ita ma tana fuskantar matsalolin ta'addanci, don haka ya zama dole Turkiyya da Najeriya da sauran kasashen duniya su hada kansu don yakar wannan matsala

Bugu da kari, shugaba Erdogan ya ce yarjejeniyar fahimtar juna da aka daddale tsakanin Turkiyya da Najeriya za ta taimaka sosai ga inganta alakar tattalin arziki da kasuwanci da karfin soji tsakanin kasashen biyu.

Sa'an nan a nasa bangaren, Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya godewa gwamnatin Turkiyya saboda kokarin da take yi na horas da 'yan sandan Najeriya, da samar da ingantattun kayan aiki don yakar ayyukan ta'addanci.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China