in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Martins ya koma kungiyar Shanghai Greenland
2016-02-19 10:43:51 cri

Dan wasan kwallon kafar Najeriya dake takawa kulaf din Seattle Sounders kwallo Obafemi Martins, ya sauya sheka zuwa kulaf din Shanghai Greenland Shenhua dake nan kasar Sin.

Da sanyin safiyar ranar Alhamis ne Martins ya shiga cikin jerin 'yan wasan kulaf din na Shanghai Greenland, domin gudanar da atisaye a garin Jeju, dake kasar Koriya ta Kudu.

Mahukuntan kungiyar sun ce suna sa ran Martins zai taimaka, wajen karfafa gaban kulaf din, da kuma samar da karin damammakin cin kwallaye.

Martins, dan shekaru 31 da haihuwa, ya tabbatar da sauyin shekar tasa a shafin sa na Twitter, yana mai cewa ya yi shirin fuskantar kalubalen dake gaban sa, bayan shafe kakar wasannin uku a Sounders.

Dan wasan na Najeriya na cikin 'yan kwallo na baya bayan nan, da suka samu gurbin taka leda a kasar Sin, kasar da a yanzu haka ke matsa kaimi wajen gayyato 'yan wasan ketare zuwa kulaflikan ta na gida, inda kuma ake biyan irin wadannan 'yan wasa baki makudan kudade.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China