in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba za a rage darajar Naira ba, in ji mataimakin shugaban Najeriya
2016-02-28 13:05:03 cri
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, ya jaddada kudurin gwamnatin kasar na kin amince da batun rage darajar kudin kasar wato Naira, duk kuwa da kiraye-kirayen da wasu ke yi game da hakan.

Osinbajo ya bayyana hakan ne jiya Asabar a birnin Ikkon jihar Legas, yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki. Ya kuma kara da cewa tuni babban bankin kasar ya fara daukar matakan daidaita musayar kudin kasar, matakan da za su dace da managarcin tsarin kudi, kamar dai yadda tuni shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya ambata.

Mataimakin shugaban kasar ya ce manufofin kudi da za a aiwatar, za su bada damar rage kudaden da kasar ke kashewa wajen shigar da kayayyaki daga ketare, tare da bunkasa sarrafa kaya a cikin kasar.

Kaza lika Mr. Osinbajo ya bayyana irin yadda a yanzu haka aka cimma nasarar rage yawan kudaden da ake kashewa wajen shigar da tacaccen mai cikin kasar, sai dai duk da hakan a cewarsa gwamnatin Najeriyar na kashe kimanin kaso 38 cikin dari na kudaden ajiyar ta na ketare, wajen shigar da tacaccen man.

Da yake tsokaci game da yadda gwamnatin da ta gabata ta tafiyar da lalitar kasar, Osinbajo ya ce gwamnatin ta baya na kashe kusan dalar Amurka miliyan 100 a kowace shekara wajen shigar da kayan abinci cikin kasar, wanda hakan ya yiwa kudaden ajiyar kasar gibi, daga dalar Amurka biliyan 40 zuwa biliyan 25.

Hakan ne kuma ya sa a cewar mataimakin shugaban Najeriya a yanzu, gwamnati mai ci ke kokarin fadada hanyoyin bunkasa tattalin arziki, da suka hada da mai da hankali ga fannin noma da na hakar ma'adanai. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China