Shugaba Buhari wanda ya fara isa birnin Riyadh a Litinin din nan ya tattauna da Sarki Salman Bin Abdulaziz Al-Saud, sannan kuma manyan jami'an masarautar a ranar Talatan nan kafin ya wuce birnin Doha a ci gaba da tattaunawar da Sarkin kasar Qatar, Sheik Tamim bin Hamad Al- Thani.
Sanarwar ta yi bayanin cewar a ci gaba da kokarin da Nigeriya take yi, a matsayin kasa mafi arzikin man fetur a nahiyar Afrika da kuma sauran mambobin kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC, ana sa ran tattauna yadda za'a samu babban daidaito na farashin danyen mai da ake fitarwa ya kasance kan gaba a tattaunawar da Shugaba Nigeriyan zai yi da takwarorin nashi.
Har ila yau ana sa ran Muhammadu Buhari zai gana da jagororin 'yan kasuwa na kasashen biyu tare da gayyatar su wajen goyon bayan gwamnatin shi a kokarin da take yi na farfado da tattalin arzikin kasar, musamman a bangaren hako ma'adinai, aikin gona, samar da wutan lantarki, ababen more rayuwa, sufuri, sadarwa da dai sauransu. (Fatimah Jibril)