A sanarwar da ma'aikatar kudin kasar ta bayar, tace an samu nasarar gano ma'aikatan na jabu ne, bayan gudanar da aikin tantance ma'aikatan, karkashin shirin yaki da rashawa da gwamnati mai ci ta bullo da shi ta hanyar tantance asusun masu mu'amala da bankunan kasar.
Ya zuwa yanzu, shirin shugaba Muhammadu Buhari na yaki da rashawa yayi nasarar rage kudaden biyan albashin kasar kimanin dalar Amurka miliyan 11 da rabi, sama da kashi 40 cikin 100 na kudaden da gwamnatin kasar ke warewa na ayyukan yau da kullum ne ke tafiya wajen biyan kudaden albashin ma'aikata.
Gwamnatin Najeriyar ta sha alwashin ci gaba da aikin tantance ma'aikatan har zuwa karshen wannan shekara, domin hakikance ainahin ma'aikatanta na hakika da suka cancanci karbar albashi a duk wata.
Wannan na daga cikin shirye shiryen da gwamnatin shugaban kasar ya bullo da shi domin yaki da rashawa da toshe hanyoyin da kudaden kasar ke zurarewa ba bisa ka'ida ba daga lalitar gwamnati, domin cike gibin kasafin kudin kasar na shekarar 2016.(Ahmad Fagam)