Kamar yadda fadar shugaban kasar ta bayyana a cikin sanarwar da ta fitar, ana sa ran shugaba Buhari zai yi jawabi a wajen taron, sannan zai yi amfani da damar wajen tattaunawa da sauran shugabannin kasashen Afrika a kan hanyar da za a bi wajen neman ci gaba a nahiyar. (Fatimah)