Mai Magana da yawun 'yan sandan kasar Joseph Kwaji, ya tabbatawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar 'yan bindigar sunyi garkuwa da Hosea Danjuma, kuma tuni aka baza jami'an sunturi na musamman domin ceto tsohon jami'in.
Steven Agya, shugaban karamar hukumar Kurmi dake jahar Tarabar ya bayayyana cewar, anyi awon gaba da mista Danjuma ne a gidansa dake Baisa da misalin karfe 1:47 na safiyar Talata.
Agya ya kara da cewar, tuni aka baza matasa a yankin domin taimakawa jami'an tsaro da nufin ceto jami'in.
Lamarin dai ya faru ne makonni biyu bayan yin garkuwa da mahaifiyar mataimakin gwamnan jahar Hajiya Beli Manu, wanda aka tsare ta na wasu sa'oi kafin daga bisani a saketa.
Batun yin garkuwa da mutane ba wani bakon abu ba ne a kasar, kuma matsalar ta fara kunno kai ne tun a shekarar 2006, inda a yankin Niger Delta aka yi garkiuwa da baki 'yan kasashen waje sama da 300 domin neman kudaden fansa.(Ahmad Fagam)