in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Palesdinu na niyyar sa kaimi ga kira taron shimfida zaman lafiya tsakanin Palesdinu da Isra'ila
2016-03-02 14:14:42 cri

Shugaban kasar Palesdinu Mahmoud Abbas ya bayyana a jiya Talata cewa, gwamnatin kasarsa za ta kara tuntubar kasashen duniya don hadin gwiwa da AL da al'ummar duniya wajen sa kaimi ga kira taron shimfida zaman lafiya tsakanin Palesdinu da Isra'ila.

Wani jami'in fadar shugaban Palesdinu ya ce, Abbas a cikin jawabin shi wajen taron kwamitin gudanarwa na kungiyar 'yantar da Palesdinu, ya bayyana fatansa na kiran wannan taro cikin lumana tare da fitar da wani tsari mai inganci don warware matsalar Palesdinu. Ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar za ta gabatar wa kwamitin sulhu na MDD wani shirin warware batun matsugunan Yahudawa cikin lokaci, don hana Isra'ila ci gaba da habaka matsugunan ta a yankin Palasdinu.

Ministan harkokin waje na kasar Faransa Laurent Fabius a nashi bangaren a wannan rana ya bayyana cewa, Faransa za ta shirya wani taro tsakanin Palesdinu, Isra'ila, Amurka, EU da wasu kasashen Larabawa don fitar da wani shirin shimfidar zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.

Ban da wannan kuma, saboda shiga tsakanin da Amurka ta yi, kasashen biyu sun farfado da shawarwari tsakaninsu daga watan Yuli na shekarar 2013, wanda aka daina shi har tsawon shekaru uku, amma ganin wasu matsalolin da ake fuskanta, an sake daina shawarwari a watan Afrilu na shekarar 2014, ciki hadda saki Palesdinawa da aka tsare, gina matsuguna da dai sauransu.

An rika tada zaune tsaye tskanin bangarorin biyu a watannin baya, inda Isra'ila ta yi suka cewa, Palesdinu ta tada da rikici, amma a nata bangare Palesdinu ta ce, dalilin aukuwar tashe-tashen hankula tsakanin su shi ne Isra'ila ta mamaye yankin Palesdinu har tsawon shekaru 50. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China