Sanarwar ta yi nuni da cewa, firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bada shawarar kafa wata kotun shari'ar harkokin jama'a don sa kaimi ga daukar matakan yanke hukunci ga Palesdinawa, kana za ta bayar da umurnin tsarewa, da rushe gidaje da dai sauransu.
Tun a karkon watan nan ne, ake fuskantar zaman dar-dar a tsakanin Palesdinu da Isra'ila. Kididdiga na nuna cewa, kimanin Palesdinawa 60 ne suka mutu a sakamakon rikicin da ya kazanta, kana mutane fiye da 2000 suka ji rauni, baya ga mutane fiye da dari daya da ka kama. A yayin da 'yan Isra'ila 11 suka mutu kana fiye da mutane 100 suka ji rauni.(Zainab)