in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gurfanar da mutanen da ake zarge da cinna wuta a kauyen Duma na Palesdinu
2016-01-04 10:31:45 cri
An gurfanar da wasu Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi su biyu, da ake zarge da cinna wuta a kauyen Duma na yankin Palesdinu gaban wata kotu dake Isra'ila.

Bisa takardar karar da aka gabatarwa kotun dake zama a yankin Lud na Isra'ila, mutanen biyu su ne Amiram Ben Uliel mai shekaru 21 da haihuwa, da kuma wani wanda bai kai shekaru 18 ba. Takardar ta zarge su da aikata laifin tada-zaune-tsaye, da haifar da husuma ga Palesdinawa, tare da daukar matakin da ka iya jawowa jama'ar Isra'ila hare-hare, wanda hakan zai canja manufar gwamnatin Isra'ila ta janye jiki daga matsugunan Yahudawa, tare da mayar da martini ga Palesdinawa.

Har wa yau kuma, a dai wannan rana, an kara gabatar da karar wasu Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi, wadanda aka zarge su da yunkurin kai hare-hare ga Palesdinawa a kotun ta Lud.

A ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2015 ne aka cinna wuta ga wani gidan Palesdinawa dake kauyen Duma, dake yammacin gabar kogin Jordan yayin da dukkan iyalan gidan ke barci, lamarin da ya haddasa mutuwar wani jariri guda, kana daga bisani kuma mahaifansa suka mutu a asibiti, yayin da wani yaro mai shekaru 4 ya ji rauni mai tsanani.

Bayan abkuwar hakan ne kuma aka fara samun tashe-tashen hankula a yankunan Isra'ila da na Palesdinu, halin da ya tsananta a watan Oktobar da ya gabata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China