in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane hudu sun mutu sakamakon fashewar nakiya a Somaliya
2016-03-02 11:20:18 cri

Rahotanni na cewa, wata nakiya da aka binne a gefen hanya a kudancin birnin Mogadishu, fadar mulkin kasar Somaliya a jiya Talata ta fashe, hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 4.

Wani jami'in gwamnatin yankin da harin ya auku, ya ce, motoci uku sun nufi yankin Afgoye a birnin na Mogadishu, lokacin da wata mota ta taka nakiyar din da aka binne a gefen hanya, matakin da sabbaba hallakar sojoji 4 nan take, yayin da wasu suka jikkata, baya ga mota da ta yi daga-daga.

Har ila yau, 'yan sanda sun cafke wani mutum da ake tuhumar da hannu cikin binne nakiyar din, kuma ana ci gaba da gudanar da aikin bincike game da aukuwar lamarin.

Kungiyar Al-Shabaab ta Somaliya ta sanar da sauke hakkin harin. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China