in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a fara aikin kwance ababen fashewa a kan iyakar Kenya da kasar Somaliya
2016-01-29 10:11:57 cri
Kasar Kenya ta aike da wata tawagar kwararru zuwa yankin Lamu dake kan iyakar kasar da Somaliya, domin fara aikin kwance ababen fashewa, wadanda mayakan kungiyar Al-Shabaab suka daddasa.

An dai dauki wannan mataki ne sakamakon yawaitar hare-haren baya bayan nan da ake kaddamarwa a yankunan Kiunga, da Baragoi, da Milimani, wadanda suka haddasa asarar rayuka da dama.

A cewar wani jami'in rundunar sojin kasar, mahukuntan Kenya sun lura da yadda mayakan kungiyar ta Al-Shabaab ke sauya salon hare-haren su, inda a yanzu suke amfani da ababen fashewa kirar hannu wajen yaki da jami'an tsaro.

A sakamakon hakan, gwamnatin kasar ta kuduri aniyar baiwa 'yan sanda damar amfani da motoci masu sulke, domin taimaka musu gudanar da ayyukan su ba tare da dogaro da rundunar sojin kasar ba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China