in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a yi fashi a tekun Somaliya a bara ba
2016-02-03 19:53:32 cri

A jiya ne hukumar kula da harkokin teku ta kasa da kasa ta bayyana a cikin rahoton da ta kaddamar na shekarar 2015 da ta gabata cewa, ba a yi fashi a tekun Somaliya ba, amma ana fuskantar barazanar da 'yan fashin tekun ke haifarwa a yankin kudancin tekun bahar Maliya wato Red Sea, mashigin tekun Aden, gabar tekun arewacin kasar Somaliya, tekun Arabiya, mashigin tekun Oman, gabar tekun gabashi da kudancin Somaliya kasar, don haka wajibi ne jiragen ruwa da ke zirga-zirga su yi taka tsan-tsan.

Kwararru na ganin cewa, sakamakon tsattsauran matakan da kasashen duniya suke dauka a shekaru huda da suka wuce, yawan matsalolin da 'yan fashi suka kai hari kan jiragen ruwa da suka yi zirga-zirga a yankin teku ya samu raguwa. Sannan wasu jiragen ruwa sun yi zirga-zirga a yankin tare da dakaru nasu masu dauke da makamai, ko kuma sun kauce wa yankin tekun Somaliya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China