in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 12 sun halaka a fashewar boma-bomai biyu a Somaliya
2016-02-27 13:10:52 cri
'Yan sandan kasar Somaliya sun bayyana a jiya jumma'a 26 ga wata cewa, an samu fashewar boma-bomai na kunar bakin wake a wani otel da kuma wani filin wasa dake birnin Mogadishu a wannan rana da dare, wadanda suka haddasa mutuwar mutane a kalla 12 tare da raunatar wassu mutane 16.

An samu fashewar bom na farko a filin wasa mai suna Peace Garden, wanda ya haddasa mutuwar mutane 7. Sannan Kuma aka samu fashewar bom na iyu a otel na SYL, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 5. Yanzu sojojin tsaron kasar Somaliya sun riga sun shiga wannan otel.

Otel din SYL dai ya na dab da fadar shugaban kasar Somaliya, kuma yawancin mutanen dake zaune a otel din jami'an gwamnatin kasar ne da sauran baki daga kasashen waje.

Kungiyar Al Shabaab ta kasar Somaliya ta sanar da daukar alhakin kai hare-haren biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China