in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka tsohon ministan tsaro na kasar Somaliya
2016-02-16 09:27:44 cri
An hallaka wani tsohon ministan tsaro na kasar Somaliya a ranar Litinin din nan 15 ga wata a birnin Mogadishu, hedkwatar kasar.

Rundunar 'yan sandan kasar ta bayyana cewa, a wannan rana, lokacin da Mohieldin Mohammed Hajj Ibrahim, wanda ya taba zama ministan tsaro na kasar Somaliya a cikin shekaru 8 da suka gabata, yake wucewa daidai wata mahadar hanya, wata mota mai dauke da bam ta fashe, abin da ya yi sanadiyar mutuwar shi nan take, ana zargin an dana na'urar tada bom din ne a cikin motarsa.

Ya zuwa yanzu dai, babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin bom. Amma, kungiyar Al-Shabaab ta Somaliya ta sha kai hare-hare da dama kamar haka a cikin 'yan shekarun nan, abun da ya haddasa mutuwar wasu manyan jami'an gwamnatin kasar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China