Kaza lika Mr. Li ya ce ana kyautata tsarin tattalin arzikin kasar ta Sin cikin kyakkyawan yanayi.
A nasa bangare, Kim Yong ya bayyana cewa, yanzu haka ana fama da matsalar tattalin arziki a duk fadin duniya, don haka kamata ya yi wasu manyan kasashe masu karfin raya tattalin arziki, su kara fidda manufofi na kyautata yanayin da ake ciki a wannan fanni. A cewar sa Sin ta canza hanyar raya tattalin arzikin ta yadda ya kamata, ta kuma gudanar da kwaskwarima bisa tsari, wanda hakan ya haifar mata da karuwar tattalin arziki cikin sauri. (Fatima)