Wang ya ce, kasashen Sin da Amurka suna da moriyar irin daya a wasu fannoni a yankin Asiya da tekun Fasific, kullum kasar Sin na bin manufar diplomasiyya ta samar da zaman lafiya da bude kofa da cimma moriyar juna a wannan yanki, kuma tana fatan ci gaba da tattaunawa tare da Amurka game da batutuwan da bangarorin biyu suka dora muhimmanci sosai a kai, ciki har da yanayin da ake ciki a teku, da inganta tuntubawa da hadin gwiwa a wannan yanki. A nasa bangaren, Haass ya ce, manyan kasashen da suke da tasiri a duniya har da kasashen Sin da Amurka sun tuntubi juna da hadin gwiwa tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, abun da zai amfanawa tinkarar kalubale a duniya da na shiyya-shiyya kuma ya dace da moriyar bangarori daban daban.
Haka kuma, a wannan rana, Wang Yi ya gana da tsohon mai ba da taimako ga tsohon shugaban kasa a fannin tsaro wato Zbigniew Brzezinski. Wang ya jinjinawa gudummawar da Brzezinski ya bayar wajen yaukaka dangantakar Sin da Amurka, kuma ya bayyana cewa kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasar Amurka don kafa dangantakar hadin gwiwa ta moriyar juna ta sabon nau'i a tsakaninsu. Ya kuma yaba da babban ci gaba da Sin ta samu, yana fata Sin za ta tashi tsaye cikin yunkurin warware manyan batutuwan duniya da na shiyya-shiyya.(Bako)