in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya gana da mai ba da taimako ga shugaban kasar ta fuskar tsaro
2016-02-25 11:32:08 cri
A ranarlaraban nan, ministan harkokin wajen Sin Wang Yi da ke ziyarar aiki a kasar Amurka ya gana da mai ba da taimako game da harkokin tsaro ga shugaban kasar Amurka Susan Rice.

Wang Yi ya ce, raya dangantakar Sin da Amurka ya dace da babbar moriyar kasashen biyu, kuma kasashen duniya suna sa ran samun hakan. Ya zama dole bangarorin biyu su bi alkiblar raya wannan dangantaka da kafa amincewar juna bisa manyan tsare-tsare da karfafa hakikanin hadin gwiwa, da daidaita sabani, don raya dangantakar don ta ci gaba da hakaba cikin sabuwar shekara.

Madam Rice a nata bangaren ta yi na'am da ra'ayin Wang Yi game da dangantakar kasashen biyu. Ta ce, Amurka tana fatan ganin ci gaba da bunkasuwar tattalin arzikin Sin, wanda ya dace da babbar moriyar Amurka, da ta kasashen duniya. Amurka tana fatan yin kokari tare da kasar Sin, don inganta yunkurin yin shawarwari game da saka jari tsakanin kasashen biyu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China