in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta iya cin gajiya daga tsarin ziri daya da hanya daya da Sin ta gabatar
2016-02-24 20:59:02 cri
Wani tsohon malamin jami'a, kuma kwararre a fannin harkokin tattalin arziki na kasa da kasa dake Najeriya Akeem Owolabi, ya ce Najeriya da sauran kasashen dake nahiyar Afirka, za su amfana daga tsarin da kasar Sin ta gabatar mai lakabin "Ziri daya da hanya daya ".

Mr. Owolabi ya bayyana hakan ne a jihar Legas dake kudancin Najeriya, yayin zantawar sa da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua a Larabar nan. Owolabi, ya kara da cewa tsarin samar da ci gaban harkokin cinikayya na kasar Sin, zai taimaka wajen bunkasa kanana da matsakaitan msana'antu a Najeriya, da ma sauran kasashen nahiyar Afirka baki daya.

Ya ce lokaci yayi da Najeriya za ta tsara manufofi, wadanda zasu ba ta damar bunkasa tattalin arzikin ta, a daidai gabar da kasar Sin ke kara maida hankali ga habaka na ta tattalin arzikin, ta hanyar fitar da hajoji zuwa kasashen waje daga masana'antun ta na gida.

Yace daukar matakai a kan lokaci ya zama wajibi, musamman duba da yadda farashin danyen mai, wanda ke samarwa Najeriyar kudaden shiga ke ci gaba da karyewa a kasuwannin duniya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China