Hua ta kara da cewa, kwanan bayan, kasar Amurka ta sha zargin kasar Sin wajen mai da harkokin tekun Nanhai a matsayin harkar soja, amma a hakika dai, kasar Amurka ba ta fadi gaskiya ba.
Hua ta ce, kasar Sin tana gudanar da aikin kiyaye tsaron kasa a yankin Nanhai yadda ya kamata, kaman irin aikin da kasar Amurka ta yi a Hawaii.
Bugu da kari, ta nuna cewa, jiragen sama na sojojin tekun kasar Amurka su kan yin bincike a yankin, lamarin yana kuma ci gaba da karuwa cikin shekaru baya bayan nan, wannan shi ne dalilin da ya haddasa tabarbarewar yanayin tsaro a yankin Nanhai, muna fatan kasar Amurka ta dakatar da yi wa kasar Sin iri wannan zargi na bai dace ba, haka kuma, ta tsayar da matakan da ta dauka a wannan yanki, kada a haddasa karin barazana ga yanayin tsaro, kaza lika, ta kuma cewa, muna fatan kasar Amurka za ta iya ba da gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya da zaman karko a yankin yadda ya kamata. (Maryam)