Cikin jawabin nata, Fu Ying, ta bayyana cewa, ana ci gaba da tattaunawa kan harkokin da suka shafi tsarin duniya a kasashen Sin da Amurka, amma, tsarin da kasashen biyu suka tattauna bai kasance iri daya ba, tsarin duniya da Amurka take tattaunawa shi ne a karkashin jagorancinta, kuma yana daukar muhimman harkoki ne guda uku, na farko ra'ayin Amurka kuma ana iya cewa ra'ayin yammacin kasashen duniya, na biyu shi ne tsarin hadin gwiwar harkokin soja, na uku shi ne hukumomin kasa da kasa dake karkashin inuwar MDD. Amma a halin yanzu ana fuskantar kalubale iri dabam dabam ta fuskar harkokin siyasa na duniya, tsarin da Amurka take tattaunawa ba zai iya warware matsalolin da ake fama da su ba a duniya.
Kaza lika, ta ce, tsarin duniya da kasar Sin take tattaunawa shi ne na bin ka'idoji dangane da harkokin kasa da kasa, da dokoki da dai sauransu bisa jagoranci na MDD.
Bugu da kari, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba gabatar da jawabi yana mai cewa, wasu kasashen duniya musamman ma kasashe masu tasowa suna sa ran raya tsarin duniya ta hanyoyin adalci yadda ya kamata. Haka kuma, kasar Sin ta samar da wasu dabaru domin warware matsalolin dake shafar tsarin duniya da ake amfani da shi a halin yanzu, sannan kiran da kasar Sin ta yi wajen kafa shirin zirin tattalin arziki na hanyar siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21 da kuma bankin zuba jari kan ababen more rayuwa na Asiya, wato AIIB su ne sabbin damammaki da kasa da kasa za su iya amfani da su.
Bugu da kari, Fu Ying ta ce, kasar Sin da Amurka suna ci gaba da samun moriya ta iri daya cikin harkokin kasa da kasa, kuma suna bukatar goyawa junan su baya wajen fuskantar kalubalen duniya, amma kasar Sin ba ta amince da tsarin duniya da kasar Amurkar ta fitar ba. (Maryam)