Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya halarci bikin bude taron manufofin samun dauwamammen ci gaban kasar Masar kafin 2030 da aka yi a birnin Alkahira, fadar mulkin kasar, yana mai kira ga majalisar dokokin kasar game da abin da ya faru a yankin Sinai, ya ce har yanzu akwai mutane da ke kokarin yiwa Masar zagon kasa, ganin yadda kasar ke fuskantar kalubalen ta'addanci a halin yanzu.
A ranar 31 ga watan Oktoban shekarar da ta wuce ce, jirgin saman kasar Rasha dauke da fasinjoji ya fadi a yankin Sinai jim kadan da tashinsa daga birnin Sharmel Sheikh, kuma dukkan mutanen 224 dake cikin jirgin sun rasu.
Bayan aukuwar hadarin, kasashen Burtaniya, Jamus, Rasha da dai sauransu sun bayyana cewa, watakila 'yan ta'adda ne suka harbor jirgin, sa'an nan, suka dakatar da jiragen saman kasashensu zuwa birnin Sharmel Sheikh.
Kana, kungiyar da ke gudanar da bincike kan hadarin da ta kunshi masana na kasashe guda biyar a karkashin jagorancin kasar Masar har yanzu ba ta bayyana rahoton bincikenta ba. (Maryam)