Makasudin dandalin da ya gudana bisa hadin gwiwar kungiyar kasuwar bai daya ta gabashi da kudancin Afirka ita ce zurfafa dangantaka tsakanin kasashen Afirka a fannonin cinikayya da zuba jari, da sa kaimi ga dunkulewar tattalin arzikin nahiyar, da jawo hankulan masu zuba jari na kasashen waje, da kuma tattauna rawar da Masar ke takawa ta fannin zuba jari a cikin bunkasuwar tattalin arzikin kasa da kasa na Afirka.
Shugabar hukumar harkokin zuba jari ta yankin COMESA, madam Heba Salama ta bayyana cewa, jimillar jarin da aka zuba a kasashen Afirka a shekarar 2015 daga ketare ta kai dala biliyan 128, wadda ta karu da kashi 136 cikin dari bisa ta shekarar 2014.
Ta ce, tattalin arzikin kasashen Afirka yana bunkasa a kai a kai ba tare da dogaro kan fitar da albarkatu zuwa kasashen waje ba. Daga shekarar 2003 zuwa 2014, kashi 38 cikin dari na jarin da aka zuba, da ayyukan zuba jari sama da kashi 50 cikin dari sun shafi sha'anin ba da hidimomi ne. A sabili da haka, ta yi kira ga kasashen Afirka da su hada kai don bunkasa tattalin arzikinsu, domin sa kaimi ga kafa wani yankin cinikayya cikin 'yanci mafi girma a Afirka.
Bikin bude dandalin ya samu halartar shugabanni da kusoshin kasashen Masar, da Sudan, da Nijeriya da wasu sauran kasashe uku, gami da jami'an gwamnatoci da 'yan kasuwa daga kasashe sama da 20, da wakilan bankin raya kasashen Afirka, da na hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin nahiyar da sauransu. Za a shafe yini biyu ana wannan taro.(Fatima)