Kaza lika rahoton ya bayyana cewa, bisa yanayin da kasuwar danyen mai take ciki a halin yanzu, ana ganin cewa ba za ta samu farfadowa cikin kankanin lokaci ba. Amma, sakamakon kasancewar adadin danyen mai na shale da Amurka ke samarwa ya ragu matuka a halin yanzu, shi ya sa ake saran zuwa shekarar 2017 za a samu daidaituwa game da farashin danyen man a kasuwannin duniya.
Bugu da kari, rahoton na ganin cewa, ko da yake a wannan shekarar ta bana da kuma shekara mai zuwa, adadin danyen mai da kasar Amurka ke samarwar zai ragu matuka, amma ya zuwa shekarar 2021 adadin zai karu zuwa ganga miliyan 14.2 cikin kowace rana, a lokacin ne ake sa ran kasuwar danyen man za ta samu tagomashi a duniya. (Maryam)