A yayin da ministan ke ziyarar aiki a garin Fatakwal na jihar Rivers da aka fi sani da rinjaye wajen fitar da man fetur na kasar Nijeriya, ya bayyana cewa, a halin yanzu, gwamnatin ba ta iya biyan rangwamen man fetur , shi ya sa, za ta soke rangwamen tun daga farkon shekarar 2016.
Kasar Nijeriya ita ce babbar kasar da ke fitar da man fetur a nahiyar Afirka, amma sabo da ba ta iya tace danyen mai sosai, shi ya sa, take sayo galibin man fetur daga kasashen ketare, lamarin da ya sa ake gamuwa da karancin man fetur a kasar a kullum. (Maryam)