in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Chadi na kamfen bunkasa arzikinta na man fetur da ma'adinai
2015-10-14 11:19:51 cri

Kasar Chadi, kasa ce dake karkashin kasarta yake kunshe da dimbin arziki dake neman a hako sa, in ji faraministan Chadi, Kalzeube Payimi Deubet a ranar Talata a yayin da aka bude dandalin kasa da kasa na man fetur, ma'adinai da makamashi na Chadi (CIOME 2015).

Kasarmu wata muhimmiyar kasa ce ta ziyarta, wato tana sahun gaba wajen dacewa da ayyukan samun moriya a bangarorin man fetur, ma'adinai da makamashi, in ji mista Kalzeube Payimi Deubet.

A tsawon kwanaki uku, Chadi za ta gabatar da arzikinta da damammakinta na man fetur, ma'adinai da makamashi ga masu zuba jari da suke fito daga duniya baki daya.

A bangaren man fetur, kasar Chadi ita ce ta goma a Afrika, tare da ajiyar gangar mai da aka kiyasta zuwa biliyan 1,5 a karkashin kasa. Wadannan arzikin ma'adanai, da har yanzu hakarsu ba ta dore ba sosai, sun hada da uranium, zinari, kanwa, da alli da sauransu.

Chadi, kasa ce mai girma a yankin Sahel, dake kuma kunshe da dimbin arzikin karfin iska, rana da na halittu.

Tawagogi da suka fito daga kasashen Guinea Equatoriale, Congo, Kamaru da Cote d'Ivoire na halartar wannan dandali na "man fetur da ma'adinai da makamashi a Chadi" karo na biyar dake gudana a lokacin da gwamnatin Chadi take fama da karancin kudi mai tsanani dalilin faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China