Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da cewar, shugaba Muhammadu Buhari na kasar zai fara ziyarar aiki ta tsawon mako guda tun daga yau Litinin a kasashen Saudiyya da Qatar domin tattaunawa game da daidaita farashin danyen mai wanda ke ci gaba da faduwa a kasuwannin duniya.
Mai magana da yawun shugaban Najeriyar Femi Adesina, ya fada a birnin Abuja, helkwatar mulkin kasar cewar, a karon farko shugaba Buhari zai yada zango ne a birnin Riyadh, domin tattaunawa da sarki Salman Bin Abdulaziz Al Saud da manyan jami'an kasar ta Saudiyya a Talata mai zuwa..
Wannan yunkuri na mahukuntan Najeriya da sauran kasashe mambobin kungiyar masu fitar da man fetur ta duniya wato OPEC, ana sa ran tattaunawar shugaba Buhari da sarkin na Saudiyya za ta samar da kyakkyawar alkibla game da daidaituwar farashin danyen man dake ci gaba da karyewa.
Sanarwar ta kara da cewar, Buhari zai gana da sarki Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani na Qatar duka dai kan batun na farashin man fetur a Lahadi mai zuwa.
Adesina ya ce, baya ga batun na mai, shugaban Najeriyar zai gana da shugabannin hukumomin kudi na kasashen duniya da kungiyoyi na kasa da kasa, da dama a kasar ta Saudiyya.(Ahmad Fagam)