A kwanan nan, kasashen Turai da Amurka suna fama da yanayin sanyi matuka, sakamakon haka, ana hasashen cewa, za su kara sayen man fetur domin dumama gidajensu, sakamakon haka, wannan ya zama wani dalilin da ya janyo karuwar farashin man fetur a kasuwa.
Ya zuwa lokacin rufe kasuwa a Jumma'a, farashin man fetur da za a mika su a watan Maris na shekarar 2016, ya karu da dalar Amurka 2.66, wato ya kai dalar Amurka 32.19 ga kowace ganga. Sannan farashin man fetur na Brent da ake sayarwa a kasuwar London ya kai dalar Amurka 32.18, wato ya karu da 10%. (Sanusi Chen)