Hukumar IEA ta yi hasashe cewa, yanzu bukatun man fetur a duniya ya ci gaba da karuwa domin farashin man fetur na duniya ya ragu sosai, Amurka da Sin da sauran kasashen duniya sun kara sayen man fetur, wanda ya sa kaimi ga samun karuwar bukatun man fetur da yawansu ya kai matsayin koli a shekaru 5 da suka gabata, wato ganga 1'800'000 a kowace rana.
A cikin rahoton, hukumar ta kiyasta cewa, yawan man fetur da za a bukata a shekarar 2016 zai ragu zuwa ganga 1'200'000 a kowace rana. (Zainab)