in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya yi waya da takwaransa na Amurka
2016-02-06 08:59:15 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi waya da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama, inda suka aika da sako da gaisuwa a yayin bikin bazara na gargajiya na Sinawa.

Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, a cikin shekarar da ta gabata, a karkashin kokarin bangarorin biyu, dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka ta samu babban ci gaba, don haka kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasar Amurka don karfafa hakikanin hadin gwiwa daga duk fannoni, da inganta mu'amala da shawarwari game da batutuwan duniya da shiyya-shiyya, don ingiza dangantakar Sin da Amurka cikin armashi.

Haka kuma, Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya, kuma tana dukufa ka'in da na'in kan yin shawarwari don warware batun, da tabbatar da zaman lafiya da karko a zirin Koriya.

Har ila yau ya ce wannan kokari na kasar Sin ya dace da babbar moriyar bangarorin da abun ya shafa, don haka Kasar za ta goyi bayan kudurorin da kwamitin sulhu na M.D.D. za ta bayar, da tsarin hana yaduwar makaman nukiliya a duniya, kuma tana fatan ci gaba da tuntubawar bangarorin da abun ya shafa ciki har da kasar Amurka.

Shi ma a nashi bangaren Shugaba Barrack Obama ya ce, ya yi farin ciki buga waya ga shugaba Xi a lokacin da ake shirin bikin bazara na gargajiya na Sinawa, kuma yana fatan alakar kasashen biyu za ta samu ci gaba.

Mr Obama ya ce Amurka ta dora muhimmanci sosai game da Koriya ta Arewa da ta yi gwajin nukiliya da wasu harbe-harbe da za ta yi, kuma yana fatan kasashen duniya su inganta yin shawarwari, don ingiza kwamitin sulhu na M.D.D. da ta dauki wasu matakai, don warware wannan batu, kasar Amurka tana fatan yin hadin gwiwa da kasar Sin game da batun.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China