in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin Sin ya bayyana ra'ayi kan shigar jirgin saman sojan Amurka a yankin sararin saman kasar Sin a kusa da tsibirin Nansha
2015-12-20 13:45:22 cri

Kafofin yada labaru na kasar Amurka sun labarta cewa, a sanyin safiyar ranar 10 ga wata, wani jirgin saman kasar na yaki kirar B-52 ya yi kuskuren ratsa yankin sararin saman kasar Sin a kusa da tsibirin Nanshan. Jami'an tsaron Amurka sun ce, jirgin ya yi haka ba bisa shiri ba ne, ya karkata hanyarsa dalilin mummunan yanayi. Amurka tana bin bahasin lamarin.

Dangane da hakan, a cewar Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin jiya Asabar 19 ga wata, kasar Sin ta sake bukatar Amurka da ta amince da kuskurenta a tsanake, ta gabatar da tubenta na yin kuskure sannan kuma ta gyara kuskuren. Kuma ta dauki matakan da suka dace wajen hana sake abkuwar irin wannan hadari, da kuma irin na tsokana, tare da daina dukkan aikace-aikacen da kawo illa ga ikon mulkin kasar Sin da moriyar Sin ta fuskar tsaro, da kuma kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin kudancin tekun kasar Sin.

Kakakin ya ce, kasar Sin tana tinkarar lamarin yadda ya kamata, ta tuntubi Amurka, inda Amurka ta ce, za ta bi bahasin batun shigar jirgin saman sojan Amurka a yankin sararin saman Sin.

Har wa yau Hong Lei ya jaddada cewa, har kullum kasar Sin na girmama da kiyaye 'yancin kasa da kasa na yin tafiya a teku da sararin sama a duk fadin duniya bisa dokokin kasa da kasa. Amma ba ta yarda da ko wace kasa da ta keta ikon mulkin kasar Sin, da kawo illa da moriyarta ta fuskar tsaro bisa hujjar yin tafiya a teku da sararin sama cikin 'yanci ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China