in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna kiyayya game da aniyar Amurka ta sayarwa yankin Taiwan makamai
2015-12-15 19:54:52 cri
A yau Talata 15 ga watan nan ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hong Lei, ya mai da martani ga aniyar Amurka, cewa gwamnatin Barack Obama na shirin shelanta amincewa da sayarwa yankin Taiwan, wasu jiragen ruwa masu dauke da makamai masu linzami, dake kare wasu jiragen guda biyu a cikin wannan mako.

Mr. Hong ya ce, Sin na matukar adawa ga wannan batu, tana kuma kalubalantar Amurka da ta cika alkawarin da ta yi, na daina sayar da makamai ga yankin Taiwan na Sin.

Rahotanni na cewa, wani mataimakin mamba a majalisar dokokin Amurka na jam'iyyar Republican ne ya bayyana niyar gwamnatin Obama, na shelanta amincewa da sayar da jiragen ruwan yakin guda biyu ga yankin Taiwan.

Wannan ne karon farko da Amurka za ta sayarwa yankin Taiwan makamai cikin shekaru 4 da suka wuce. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China