in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya yi magana da takwaransa na Amurka ta wayar tarho
2015-12-14 15:59:31 cri
A yau Litinin 14 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi magana da takwaransa na Amurka Barack Obama ta wayar tarho.

A yayin hirar tasu, shugaba Xi ya bayyana cewa, bisa kokarin kasa da kasa, an zartas da yarjejeniyar Paris a gun babban taron sauyin yanayi na MDD, wanda za ta gabatar da hanyar da za a bi wajen yin hadin gwiwa kan tinkarar sauyin yanayi bayan shekarar 2020. Wannan ne batu mai ma'ana sosai, wanda zai kawo alheri ga jama'ar kasa da kasa baki daya. Sin da Amurka da kuma sauran kasashen duniya suna mu'amala da juna, tare da ba da gudummawa sosai wajen cimma nasarar babban taron Paris. Kuma taron Paris zai zama wani masomi na yin hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya a fannin tinkarar sauyin yanayi. Sin na fatan yin hadin gwiwa da Amurka da sauran kasashen duniya, domin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar Paris yadda ya kamata, da zurfafa hakikanin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a wannan fanni, ta yadda za a kara kawo alheri ga jama'ar Sin da ta Amurka, har ma ga bil'adam baki daya.

A nasa bangare, shugaba Barack Obama ya ce, Amurka na fatan yin kokarin tare da Sin da ma sauran kasashen duniya, domin tabbatar da aiki da yarjejeniyar. Mu'amala da hadin gwiwa tsakanin Amurka da Sin a fannin tinkarar sauyin yanayi na sheda cewa, kasashen biyu na iya yin hadin gwiwa tsakaninsu cikin harkokin duniya iri iri.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China