in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwalejojin Confucius sun kara bunkasa dangantakar Sin da Afirka, inji wani masanin Afirka ta kudu
2016-02-19 10:23:22 cri
Jami'in gudanarwar kwalejin Confucius na jami'ar Johannesburg ta kasar Afirka ta kudu David Monyae, ya bayyana cewa, kwalejojin Conficius suna taimakawa wajen kara bunkasa hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka.

Jami'in wanda ya bayyana hakan yayin da ya ke jawabi ga jami'an diflomasiya da na gwamnati da kuma malaman jami'o'i a birnin Pretoria, ya ce , an kafa kwalejojin ne domin jama'a su kara fahimtar kasar Sin sannan al'ummar Sinawa su ma su kara fahimtar nahiyar Afirka.Bugu da kari, wata kafa ce ta kara fahimtar akidojin Confucius sannan a kwatanta su da akidun Ubuntu dake yankin kudancin Afirka.

David Monyae ya kara da cewar, kwalejojin sun kara samar da wata dama ga kasar Sin wajen daukar nauyin gudanar da wasu muhimman ayyuka a nahiyar Afirka da cimma nasarar raya harkokin siyasa da tattalin arzikin kasashen Afirka.

Ya kuma bayyana cewa, dangantakar Sin da kasashen na Afirka ta wuce ta sanya hannu kan yarjejeniyoyi da ziyarce-ziyarce tsakanin manyan jami'ansu. Yana mai cewa, kasashen biyu suna da dogon tarihi na hadin gwiwar abokantaka.

Monyae ya ce, kasar Sin ta taimakawa gwagwarmayar neman 'yancin kasashen Afirka ta hanyar samar da horo da makamai a kasashen Afirka ta kudu da Zimbabwe da sauransu, baya ga Sinawa da dama da suka rasa rayukansu a lokacin da suke taimakawa al'ummar Afirka gina hanyar layin dogo ta TAZARA tsakanin Zambia da Habasha.

Ya ce, a takaice dai kwalejojin na Conficius suna bayyana tarihi da labarin Sinawa ne a zahiri, ta yadda al'ummar duniya za ta kara fahimtar abin da ake nufi da kasar Sin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China