in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakon shugaban kasar Afrika ta kudu game da sabuwar shekarar Sinawa
2016-02-06 12:26:43 cri
Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacon Zuma a ranar Jumma'a nan ya mika sakon fatan alheri ga daukacin al'ummar Sinawa dake kasarsa da ma duniya baki daya, yana mai masu fatan samun farin ciki da ci gaba a sabuwar shekarar, wato shekarar biri.

Ya ce Biri dabba ne ake ma gani yana da ma'anar ci gaba don haka wannan shekarar ana fatan kara samun ci gaba, samar da sabbin fasahohi, kirkiro da wassu damammaki da alheri a cikin kasuwanci da za'a yi.

Babu shakka, dole ne shekarar biri ta karfafa tare da murnar ci gaban sana'o'in mutane, kafa burin da ake son cimmawa cikin tabbaci da kuma samun nasara a sakamakon nacewa da imanin da ake da shi, in ji shugaba Zuma.

Ya ce zumuncin dake tsakanin kasashen Sin da Afrika ta kudu ya kara ci gaba, wanda ya ce za'a iya cewar alamar biri ya kama karfin zumuncin ya kara mashi kuzari da ingiza shi ta yadda zai mai da hankali a kan samun ci gaban burin da aka sa a gaba.

A karatowar wannan sabuwar shekara ta Sinawa, lokaci ya yi da za'a yi nazarin shirin da burin da ake da shi a shekara mai kamawa.

Ya ce lokaci ne mai muhimmanci na kafa burin da ake da shi domin zumuncin dake tsakaninsu, sannan ya yi kira tare da ba da kwarin gwiwwa ga daukacin Sinawa mazauna kasar Afrikan ta kudu da su kara samar da kafofin ayyuka ta kafa da kuma ingiza ci gaba kananan ma'aikatunsu ko ma kasuwancinsu don ya zama daya daga cikin burin da ake fatan cimmawa a sabuwar shekarar da za'a shiga.

Shugaba na kasar Afrika ta kudu ya ce a matsayinsu na 'yan kasa, sun yaba matuka a kan rawar da al'ummar Sinawa suke ci gaba da takawa a kowace rana a rayuwan kowane dan kasa. Saka jarin da suke yi, samar da ayyukan yi a daukacin fadin kasar a wuraren da suke aiki, ya taimaka gaya na samar da rayuwa mai inganci ma duk wanda ke zaune a kasar. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China