in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata sassa daban daban na Syria su ci gaba da kokarinsu na yin shawarwari
2016-02-04 20:33:03 cri

Manzon musamman na MDD mai kula da batun Syria Staffan de Mistura ya shaidawa taron manema labarai cewa, an dakatar da shawarwarin zaman lafiya game da kasar Syria har zuwa ranar 25 ga watan Febrairu.

Dangane da lamarin, Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Alhamis a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, duk da matsalar da aka fuskanta game da shawarwarin zaman lafiyar, hanya daya kacal ta warware matsalar kasar Syria ita ce yin shawarwari. Don haka wajibi ne sassa daban daban na kasar su hada kai domin ci gaba da shawarwarin.

Ya kara da cewa, shawarwarin zaman lafiya na wannan zagaye, wani kyakkyawan mafari ne, inda gwamnatin Syria da masu adawa suka koma kan teburin shawarwari bayan shekaru 2. Matsalar Syria mai cike da sarkakkiya ta dauki tsawon shekaru tana adabar mutane. Duk da matsalolin da aka fuskanta a karon farko na kaddamar da shawarwarin zaman lafiyar, Kamata ya yi bangarori 2 da ke yin shawarwari tsakaninsu su dauki matakai a kokarin inganta amincewa da juna, kana su taimaka wa manzon musamman na MDD, wanda ke kokarin shiga tsakani, a yunkurin ganin an ciyar da shirin siyasar Syria gaba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China