in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya halarci taron samar da gudummawar jin kai ga Syria karo na 4
2016-02-05 10:41:53 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci taron samar da gudummawar jin kai ga Syria karo na 4, taron da ya gudana jiya a birnin London.

A jawabinsa a gun taron ya bayyana cewa, Sin tana nuna goyon baya ga taron da aka shirya, yana fatan za a yi amfani da wannan taro don cimma burin shimfida zaman lafiya da sassauta halin jin kai a kasar Syria.

Ya kuma bayya cewa, kamata ya yi a hanzarta warware matsalar jin kai da kasar Syria ke fuskanta daga tushe, kuma akwai bukatar a kula da rayuwar 'yan gudun hijira da wadanda suka rasa gidajensu a kasar Syria. Bugu da kari, ya kamata bangarori daban daban na kasar Syria su aiwatar da kudurin da kwamitin sulhun MDD ya tsara, da bude hanyoyin shigar da kayayyakin jin kai da tabbatar da yin jigilar su cikin lokaci.

Har ila yau kamata ya yi kasashen duniya su samar da gudummawar jin kai ga kasar Syria da kuma kasashen da ke karbar 'yan gudun hijirar kasar Syria.

Wang Yi ya yi nuni da cewa, kamata ya yi kasashen duniya su kara yin kokari don ingiza yunkurin warware matsalar kasar ta Syria ta hanyar siyasa, wannan shi ne tushen warware rikicin jin kai a kasar Syria. Kana Sin tana goyon bayan MDD da ta yi kokarin shiga-tsakani kan wannan batun, da yin kira ga kasa da kasa da su taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga bangarori daban daban na kasar Syria da su cimma daidaito don hanzarta komawa teburin yin shawarwarin shimfida zaman lafiya a birnin Geneva.

Wang Yi ya sanar da cewa, gwamnatin kasar Sin za ta kara samar da gudummawar hatsi ton dubu 10 ga kasar Syria don sassauta matsalar karancin abinci da 'yan gudun hijira na kasar Syria suke fuskanta.

A karshe, Wang Yi ya bayyana cewa, Sin za ta ci gaba da samar da gudummawa ga jama'ar kasar Syria ciki har da 'yan gudun hijirar kasar Syria dake kasashen waje, da ci gaba da samar da taimako wajen warware rikicin jin kai na kasar ta Syria, da kuma taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga warware rikicin kasar Syria ta hanyar siyasa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China