Wang Yi ya jaddada cewa, Sin ta yi kira ga gwamnatin kasar Syria da kungiyoyin 'yan adawar kasar da su ba da muhimmanci ga moriyar jama'ar kasar Syria. Ya ce, kamata ya yi su halarci shawarwarin zaman lafiyar kasar ba tare da gindaya wani sharadi ba, da sa kaimi ga yin shawarwarin shimfida zaman lafiya sannu a hankali, ciki har da batutuwan amincewa da shigar da kayayyakin jin kai a kasar, da tsagaita bude wuta da dai saurausu, ta haka ne za a imance da juna sannu a hankali.
Wang Yi ya kara da cewa, a kwanakin baya, bi da bi ya gana da wakilan gwamnatin kasar Syria da na kungiyoyin 'yan adawa a birnin Beijing, inda ya yi kokarin shawo kansu da su halarci taron shawarwarin shimfida zaman lafiya na kasar. (Zainab)