Ministan watsa labaru na kasar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary ya shelanta cewa, daga ranar 11 zuwa 14 ga wata, sojojin kasar sun harbe 'yan kungiyar Boko Haram 162, tare da lalata cibiyoyin samar da makamai da kuma makamansu da dama. Dadin dadawa, sojojin sun kwace garin Goshi dake arewa maso gabashin Najeriya daga hannu mayakan kungiyar. Yanzu haka garin yana hannun sojojin Najeriya.
Mista Bakary ya furta cewa, sojojin Kamaru sun ceto mutane kimanin 100 da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi garkuwa da su.
Bugu da kari,minisan ya ce, an gudanar da wannan aiki ne tare da hadin gwiwar Nijeriya. Kuma sojojin Kamaru biyu sun rasu a lokacin wannan fafatawa.(Fatima)