Daya daga jiragen biyu dai ya tashi ne dauke da ministan sufurin kasar ta Kamaru Edgard Alain Mebe Ngo'o, da jakadan kasar Sin dake Kamarun Wei Wenhua, da mataimakin shugaban kamfanin Avic, kamfanin da ya kera jiragen Mr. Xu Bo, da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar da kuma manyan 'yan kasuwa.
Bayan kammala kaddamar da jiragen, ministan sufurin kasar ta Kamaru ya bayyana gamsuwa da ingancin jiragen. Kaza lika Mr. Mebe Ngo'o ya bayyana cewa cikin watan Maris mai zuwa, jiragen za su fara jigilar fisinjoji kamun da na'in.
A nasa tsokaci Mr. Xu Bo, ya bayyana cewa jiragen kirar MA60 suna iya tashi da sauka a kananan filayen jiragen sama, suna kuma da nagarta irin ta sabbin samfurin jirage na zamani.
Da zarar sun fara daukar fasinja, jiragen za su rika tashi zuwa Gabon, da Equatorial Guinea, da janhuriyar Afirka ta tsakiya da kuma kasar Chadi.
A nasa tsokaci yayin bikin, jakadan kasar Sin a Kamaru Wei Wenhua, ya ce irin hadin gwiwar da kasar Sin ke yi tare da Kamaru, ya nuna fatan da ake da shi na bunkasa safarar jiragen sama a tsakanin kasashen Afirka, musamman ta hanyar bunkasa samar da managartan jirage, da horas da ma'aikata, da samar da fasahohi tare da ginin manyan ababen more rayuwa.




