in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin Bam ya hallaka mutane 13 a yankin arewa mai nesa na kasar Kamaru
2016-01-13 20:07:48 cri
Ministan watsa labarai na kasar Kamaru Issa Tchiroma Bakary, ya tabbatar da rasuwar mutane a kalla 13, sakamakon wani harim Bam da aka kai a yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru.

Bakary wanda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua hakan, ya ce lamarin ya auku ne da Asubahin wannan Laraba, a wani masallaci dake kauyen Kouyape, a yankin na arewa mai nisa.

Mayakan kungiyar Boko Haram mai sansani a Najeriya dai sun sha kaddamar da makamancin wannan hari a kasar ta Kamaru.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China