Wata majiya daga rundunar sojin kasar ta shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, wasu mata ne su biyar dake tallar kayan marmari suka boye ababan fashewar a cikin kwandunan da suke tallar, inda suka tada bama baman da misalin karfe 11:30 na safe wanda ya yi daidai da karfe 10:30 agogon GMT a ranar Litinin a kauyen Bodo, dake yankin arewa mai nisa, harin wanda ya kashe mutane 35 ciki har da maharani, sannan ya jikkata mutane 60.
Sai dai ana zargin mayaka masu kaifin kishin Islama na Boko Haram da kaddamar da wannan harin.
Jamhuriyar Kamaru ta fara fuskantar hare haren kungiyar Boko Haram ne tun daga shekarar 2013, kuma ya zuwa yanzu, sama da mutane dubu 1 ne hare-haren ya yi sanadiyyar mutuwarsu. (Ahmad Fagam)