Ministan sadarwa na kasar Kamaru Issa Tchiroma Bakary ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar na cewar kungiyar boko haran ta kaddamar da hare hare sau 315, harin kunar bakin wake sau 32 sannan harin dashen nakiyoyi guda 12 tun daga shekara ta 2013 a yankin arewa mai nisa na kasar.
Daga cikin mutanen da aka hallaka a cikin harin akwai fararen hula 1,098, sojoji 67 da 'yan sanda guda 3 inji sanarwar.
A ranar laraba ne wadansu da ake zargin 'yan kungiyar ta boko haram ne suka hallaka a kalla mutane 13 a wani harin kunar bakin wake a yankin na arewa mai nisa.