Mutane 11 sun mutu a cikin wani harin kunar bakin wake a Kamaru
A kalla mutane goma sha daya ne aka tabbatar sun mutu kana kusan talatin suka jikkata a lokacin da wasu tagwayen hare haren kunar bakin wake suka faru a ranar Laraba da safe a Nguetchewe dake yankin kuriyar arewacin Kamaru mai iyaka da tarayyar Najeriya, a cewar wasu majiyoyin tsaro. Wasu mata 'yan kunar bakin wake biyu ne suka tada bama bamai da suke dauke da su a yayin wani zaman makoki da misalin karfe biyar da rabi na safe bisa agogon wurin, lamarin da nan take ya halaka mutane shida, har ma da 'yan kunar bakin waken biyu, tare da raunana mutane talatin, kuma wasu daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali, in ji wadannan majiyoyi. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku