Harin ya abku ne a lokacin sallan asuba a wani masallaci dake kauyen Kouyape a yankin na arewa mai nisa wanda ake zargin 'yan kungiyar boko haram ne suka kai shi.
Magatakardan ya jaddada kiran shi na a cikin tsanaki a nemi hanyar da za'a ga cewar an hana afkuwar hakan nan gaba da kuma hana yawaitan harin ta'addanci , binciko dalilan faruwan su bisa ka'idodjin jin kai na duniya da hakkin bil adama da ma dokar 'yan gudun hijira kamar yadda sanarwar da Kakakin Ban ki Moon din ya fitar.
Mr Ban ya kuma bukaci da a ba babban taron hada gudunmuwa na kungiyar kasashen Afrika goyon baya wanda za'a yi a ranar 1 ga watan Fabrairu mai zuwa domin hada kudade na rundunar hadin gwiwwa da zummar yakan ta'addancin kungiyar boko haram.(Fatimah Jibril)