Kasar Sin ta gano Koriya ta Arewa ta harba wani tauraron dan Adam, kuma tana sanya ido kan ra'ayoyi na bangarorin da abin ya shafa.
Haka kuma, kasar na ganin cewa, ko da yake, Koriya ta Arewa tana da ikon yin amfani da sararin samaniya cikin lumana, amma a halin yanzu, ana hana ta aiwatar da ikonta game da wannan batu bisa tsarin kwamitin sulhu na MDD, shi ya sa, kasar Sin ta bayyana bakin cikinta bisa matakin da Koriya ta Arewa ta dauka na sabawa gamayyar kasa da kasa, domin harba tauraron dan Adam da fasahar makamai mai linzami.
Bugu da kari, ta ce, kullum kasar Sin na ganin cewa, za a iya shimfida zaman karko da zaman lafiya na dindindin a yankin Koriya ta hanyar yin shawarwari. Shi ya sa, ya kamata bangarorin da abin ya shafa su fara yin shawarwari a tsakaninsu tun da wuri, domin kaucewa tabarbarewar yanayi a wanan yankin. (Maryam)