Kamar yadda sanarwar da ofishinta ya fitar an yi ganawar gaggawa bayan da makwabciyar ta Koriya ta Arewa ta kaddamar da roka misalin karfe tara da rabi na safiyar wannan rana daga tashar rokarta a Tongchanr-ri dake gabar yamma.
Madam Park ta ce kasar Koriya ta arewar ta inganta fasahar makamanta na linzami domin dalili daya kawai na ci gaba da mulkinta, tana mai kiran wannan kaddamarwar a wani kalubale ga kasashen duniya ganin yadda aka yi shi lokacin da kwamitin tsaron MDD ke cikin tattaunawar yuwuwar samar da sabbin takunkumi a kan kasar dangane da gwajin makaman Nukiliya da ta yi karo na 4. (Fatimah Jibril)