Mista Hong ya fadi haka ne a gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, yayin da yake mai da martani ga batun shigowar wani jirgin saman yakin mallakar Amurka samfuri B-52 cikin zirin Koriya.
A daya bangaren kuma an labarta cewa, rundunar sojan Koriya ta Kudu ta farfado da yayata farfaganda da take gudanarwa da amsa kuwa kan kasar Koriya ta Arewa a kan iyakar kasashen biyu.
Game da wannan batu, Mr. Hong ya bayyana cewa, Sin na tsayawa tsayin daka wajen ba da kariya ga tsarin hana bazuwar makaman nukiliya a duniya, da rashin yarda da gwajin nukiliya da kasar Koriya ta Arewa ke yi. Kaza lika kasar ta Sin na fatan yin mu'amala da bangarori daban daban, a kokarin ta na sa kaimi ga farfado da shawarwari tsakanin su game da batun nukiliya a zirin Koriya, ta yadda za a cimma burin kawar da makaman nukiliya a zirin, tare da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a arewa maso gabashin nahiyar Asiya cikin hanzari.(Fatima)